Acts 3

1Sa’adda Bitrus da Yahaya suna hanya zuwa haikali a lokacin addu’ar karfe uku. 2Wani mutum, gurgu ne tun daga haihuwa, ana daukar sa kulluyomi zuwa kofar haikali da ake kira Kyakkyawa, domin bara gun mutanen da ke shiga haikalin. 3Da ya ga Bitrus da Yahaya suna shiga haikalin, sai ya roke su sadaka.

4Bitrus da Yahaya kuwa suka zuba masa ido, Bitrus ya ce, ‘’Ka dube mu.‘’ 5Gurgun nan kuwa ya dube su, yana tsammanin zai sami wani abu a wurin su. 6Amma Bitrus ya ce, “Azurfa da Zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, zan baka. A cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, Yi tafiya‘’

7Bitrus ya kama hannun damarsa, ya daga shi; nan da nan kafafunsa da kashin idon sawayensa suka samu karfi. 8Da gurgun ya yunkura, ya mike tsaye sai ya fara takawa; ya shiga haikali tare da Bitrus da Yahaya, yana takawa, yana tsalle, yana kuma girmama Allah.

9Dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana kuma yabon Allah. 10Sun lura cewa, shine mutumin da ke zama yana bara a Kyakyawar kofar haikali; sai suka cika da mamaki domin abin da ya faru.

11Yayin da yake rike da Bitrus da Yahaya, dukan jama’a suka matso wurinsu, a gefen dakalin Sulaimanu, suna ta mamaki kwarai. 12Da Bitrus ya ga haka ya amsa wa jama’ar, “Ya ku mutanen Isra’ila, don me ku ke mamaki?” Don me ku ka zura mana ido, kamar mu ne muka sa shi ya yi tafiya da ikon kanmu ko adalcin mu?

13Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allah na iyayenmu ya girmama bawansa Yesu. Shi kuka ki kun kuma bashe shi a gaban Bilatus da ya so ya sake shi. 14Kuka ki Mai Tsarkin nan, Mai Adalcin, maimakon haka kuka ce a sakkar maku mai kisan kai.

15Kun kashe mai ba da rai, wanda Allah ya tayar daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga wannan al’amari. 16Yanzu, ta bangaskiya ga sunansa - wannan mutum da kuke gani kuma kun san shi - ta wurin wannan sunan ne ya sami karfi. Bangaskiya cikin Yesu ta ba shi cikakkiyar lafiya, a gabanku duka.

17Ya ku ‘yan’uwa, na san kun yi haka ne cikin rashin sani, yadda shugabaninku suka yi. 18Amma duk abubuwan da Allah ya fada ta bakin dukan anabawansa, cewa Almasihunsa zai sha wahala, yanzu ya cika.

19Saboda haka, Ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, domin lokacin sabuntuwa daga wurin Ubangiji ya zo; 20domin a aiko maku da Almasihu wanda aka kaddara wato, Yesu.

21Shine wanda dole sama ta karbe shi har zuwa lokacin komo da dukan abubuwa, game da abubuwan da Allah ya fada tun da ta bakin annabawansa tsarkaka. 22Musa hakika ya ce, ‘Ubangiji Allah zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin, ‘yan’uwanku. Za ku saurari dukan abin da zai fada maku. 23Zai kasance kowanne mutum da bai saurari annabin nan ba za a kau da shi gabadaya daga cikin mutanensa.’

24I, dukan annabawa tun daga Sama’ila da wadanda suka zo bayansa, sun yi magana sun ambaci wadannan kwanaki. 25Kune ‘ya’yan annabawa da na alkawari wanda Allah ya yi da kakanninku, yadda ya ce wa Ibrahim, ‘Daga zuriyarka dukan al’uman duniya za su sami albarka.’ Bayan da Allah ya ta da bawansa, a gareku ne ya fara aiko shi, domin ya albarkace ku tawurin juyadda kowannenku daga muguntarsa.”

26

Copyright information for HauULB